Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kura Ta Lafa A Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya... - 2002-10-29


An bada rahoton lafawar kura a Bangui, babban birnin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, a bayan da aka shafe kwanaki hudu cur ana bai wa hammmata iska a tsakanin sojojin 'yan tawaye da masu yin biyayya ga gwamnati.

Lafawar kurar ta biyo bayan gwabzawar da aka yi cikin dare a ciki da kuma kewayen fadar shugaban kasar a tsakiyar birnin Bangui. Wasu rahotanni sun ce 'yan tawaye sun dirkaki gidajen rediyo da telebijin na gwamnatin kasar.

Har yanzu ba a san inda shugaba Ange Felix Patasse ya ke ba.

Magoya bayan tsohon babban hafsan sojojin kasar, Francois Bozize (Bow-zii-zey) sune suka kaddamar da wannan tawaye ranar Jumma'ar da ta shige a wani yunkuri na hambarar da gwamnatin shugaba Patasse. Sojojin 'yan tawaye, wadanda ke samun goyon bayan sojoji daga Chadi, makwabciyarsu, suna rike da kashi guda cikin uku na birnin Bangui.

Sojoji da jiragen saman yakin Libya suna taimakon sojojin gwamnati. Har ila yau, akwai wasu rahotannin da ba a tabbatar ba dake cewa sojoji daga Kwango Kinshasa suna dafawa gwamnati a wannan fadan.

Ba a san yawan mutanen da suka mutu ba a wannan fada. Dubban fararen hula dai sun gudu daga gidajensu.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, MDD, Kofi Annan, yayi tur da yunkurin juyin mulkin, ya kuma yi kira ga 'yan tawayen da su kawo karshen wannan tunzuri.

XS
SM
MD
LG