Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Colombia Ya Hana Sakin Giggan Fataken Muggan Kwayoyi - 2002-11-03


Shugaban kasar Colombia, ya sa kafa ya shure umurnin da wani alkali ya bayar na sako wasu giggan fataken hodar iblis ta Cocaine na garin Cali, tun lokacin da aka yanke musu na dauri a kurkuku bai cika ba.

Shugaba Alvaro Uribe ya ce ya hana sako mutanen ne a saboda tababa game da sahihancin wannan hukumci da alkalin ya yanke a shari'ance ranar Jumma'a, cewar a sako Miguel Rodriguez da Gilberto Rodriguez bayan da suka shafe rabin wa'adinsu kawai a gidan kurkuku.

A ranar Jumma'a, alkali Pedro Jose Suarez, ya ce ana iya sako wadannan 'yan'uwa tun kafin cikar wa'adinsu a saboda halayyan kirki da suka nuna a daure.

An kama mutanen biyu a shekarar 1995, daga baya aka yanke musu hukumcin daurin shekaru 15 a kurkuku saboda safarar hodar iblis ta Cocaine zuwa Amurka.

XS
SM
MD
LG