Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Burundi Sun Kashe 'Yan Tawaye Fiye Da Hamsin Kusa Da Babban Birnin Kasar - 2002-11-03


Rundunar sojojin Burundi ta ce ta kashe 'yan tawaye su akalla 51 a kusa da Bujumbura, babban birnin kasar.

Rundunar ta ce an hallaka wadannan 'yan tawaye a bayan da aka wuni ana gwabza fada jiya asabar a wani kauye mai tazarar kilomita 50 a arewa da babban birnin. Wani kakakin rundunar sojojin ya ce an gice da gwabza fada a bayan da 'yan tawaye su kimanin 200 zuwa 300 suka tsallaka cikin Burundi daga Kwango Kinshasa.

A wani lamarin dabam da ya faru jiya asabar da daddare kuma, rundunar sojoji ta ce 'yan tawaye sun kashe sojojin gwamnati biyu a arewa maso yamma da birnin Bujumbura.

An kashe mutane kimanin dubu 250 a yakin basasar da ake gwabzawa a Brundi a tsakanin 'yan tawayen kabilar Hutu, da rundunar sojojin kasar wadda 'yan kabilar Tutsi suka kanainaye.

A yanzu haka, wakilan kungiyoyin 'yan tawaye suna tattaunawa kan tsagaita wuta da jami'an gwamnati a kasar Tanzaniya, to amma wasu bangarorin 'yan tawayen sun ki shiga cikin tattaunawar.

Yaki ya barke a kasar Burundi cikin watan Oktobar shekarar 1993, a bayan da sojojin laima 'yan kabilar Tutsi suka kashe shugaban kasar na farko da aka taba zaba ta hanyar dimokuradiyya, kuma dan kabilar Hutu.

XS
SM
MD
LG