Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Binne Mutanen Da Suka Mutu A Girgizar Kasa A Italiya - 2002-11-03


Mazauna wani kauye a yankin kudancin Italiya, sun binne mutane 29 da suka mutu a girgizar kasar makon jiya, wadda ta lalata wata makaranta ta kashe dukkan daliban aji daya masu shekaru shida-shida da haihuwa.

Shugaba Carlo Azeglio Ciampi da matarsa sun halarci wurin jana'izar mutanen da aka yi yau lahadi a kauyen San Giuliano di Puglia, mai tazarar kilomita 225 a kudu maso gabashin birnin Rum.

Dalibai 26 da malami guda sun mutu cikin makarantar, wadda ta ruso kansu lokacin wannan girgizar kasa ta ranar alhamis. Wasu mutanen biyu sun mutu cikin wannan kauye.

An kaddamar da bincike domin gano ko za a iya tuhumar wani ko wasu da laifin sakaci saboda rushewar wannan ginin makaranta.

XS
SM
MD
LG