Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zabe Yau Lahadi A Kasar Turkiyya - 2002-11-03


Turkawa suna jefa kuri'a a babban zabe na kasa da ake kyautata zaton zai haifar da gagarumin sauyi a majalisar dokoki da kuma gwamnati, a bayan da aka shafe kusan shekaru biyu ana fama da rikicin tattalin arziki da na siyasa.

Dukkan jam'iyyu guda ukun da suke gudanar da mulki yanzu haka a kasar Turkiyya suna iya waye gari ba tare da samun ko da kujera kwaya daya tak ba a sabuwar majalisar dokokin da za a zaba. Kuri'un neman ra'ayoyin jama'a sun nuna cewa ba zasu samu kashi goma cikin 100 da ake bukatar kowace jam'iyya ta samu kafin ta hau kan wata kujera a majalisar dokoki ba.

Jam'iyyar da take kan gaba a kuri'un neman ra'ayoyin jama'a ta samo asalinta daga wata jam'iyyar Islama da aka haramta. Amma kuma shugaban Jam'iyyar ta Adalci da Raya Kasa, kuma tsohon magajin garin birnin Istanbul, Recep tayyip Erdogan, ba zai iya azama firayim minista ba, kuma ba zai iya shiga majalisa ba, a saboda an taba samunsa da laifin karanta wani baitin wakar da hukumomi suka ce na neman tayar da fitina ne lokacin wani gangamin siyasa.

Jam'iyyar da ke ta biyu kuma, ta 'yan gurguzu ce mai ra'ayin kawar da addini daga cikin harkokin mulki.

Masu fashin bakin siyasa suka ce al'ummar Turkiyya sun kufula da abinda suke gani a zaman zarmiya da rashin iya gudanar da aiki na 'yan siyasar dake mulkin kasar a yanzu.

Ita jam'iyyar da take kan gabar, duka-duka shekara daya tak da kafa ta.

XS
SM
MD
LG