Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Amince Da Sabon Gwajin Da Zai Gano Cutar Kanjamau Cikin Mintoci 20 Kawai - 2002-11-08


Jami'an lafiya na Amurka sun ce da wani sabon gwaji mai sauki na jini, wanda zai gano kwayar cutar kanjamau ta AIDS cikin mintoci 20 kawai, maimakon jiran kwana da kwanaki, wani lokaci har na makonni.

Ana iya gudanar da wannan gwaji kusan a ko'ina, kuma sakamakonsa yana da saukin ganewa.

Ana yin wannan gwaji ta hanyar samun digon jini guda daya tak, wanda ake sanyawa cikin kwalbar dake dauke da wani ruwan magani dake canja launi idan akwai kwayar cutar kanjamau a ciki.

Jami'an lafiya na Amurka suka ce a kashi 99 daga cikin 100 na lokuta, gwajin yana nuna sakamako na gaskiya, kuma ba ya da tsada.

Suka ce suna fatan wannan zai sa a samu karin mutanen da zasu gabato domin gwajin cutar, tare da dakile yaduwarta.

Wadanda suka kirkiro da sabuwar hanyar gwajin sun ce suna fatar sayar da kayan gwajin sosai a fadin nahiyar Afirka, inda ake fama da mummunar matsala ta yaduwar cutar AIDS.

XS
SM
MD
LG