Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nijeriya Ta Ce Kotuna Ba Su Da Ikon Yanke Hukumcin Kisa Ta Hanyar Jefewa - 2002-11-10


Gwamnatin Nijeriya ta ce idan har bukatar haka ta taso, zata hana kotunan Shari'ar Musulunci na kasar aiwatar da hukumcin kisa ta hanyar jefewa.

Wata sanarwar da aka bayar a Abuja, babban birnin kasar, ta ce gwamnatin ta Nijeriya tana goyon bayan 'yancin da kotuna suke da shi na gudanar da ayyukansu ba tare da tsoma bakin gwamnati ba, amma kuma gwamnatin tarayya zata yi amfani da ikon da tsarin mulki ya ba ta domin tabbatar da cewa babu wanda aka kashe ta hanyar jefewa.

Karamin ministan harkokin wajen Nijeriya, Dubem Onyiam, ya ce gwamnati zata tsoma baki ta hana gudanar da irin wannan hukumcin kisa a bisa dalilai na kare hakkin bil Adama, domin hana al'ummarta daga shan bakar wahala.

Kotunan Shari'ar Musulunci a arewacin Nijeriya sun yanke hukumcin kisa ta hanyar jefewa kan mutane akalla hudu wadanda aka samu da laifin zina ko kuma fyade. Har yanzu babu daya daga cikin wadannan hukumce-hukumce da aka zartas a saboda daukaka kara.

Kasashe da dama sun ce zasu kauracewa bukin gasar sarauniyar kyau ta duniya da aka shirya gudanarwa a Abuja ranar 7 ga watan Disamba, a saboda rashin jin dadinsu game da wannan hukumci na jefewa.

XS
SM
MD
LG