Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Ivory Coast Sun Ki Yarda Da Shirin Zaman Lafiya... - 2002-11-14


'Yan tawayen Ivory Coast sun ce zasu ci gaba da zama a wurin shawarwarin neman zaman lafiya a Lome, babban birnin Togo, duk da cewa sun sanya kafa sun shure daftarin shirin cimma zaman lafiyar da masu shiga tsakani na Afirka ta Yamma suka gabatar.

A lokacin da suke yin watsi da shirin, 'yan tawaye sun ce wannan daftari yana nuna goyon bayan gwamnatin shugaba Laurent Gbagbo, kuma zai kyale shi ya ci gaba da mulki. 'Yan tawayen dai sun bukaci da a gudanar da sabon zabe, abinda gwamnati ta ce ba zai yiwu ba.

'Yan tawayen sun gabatar da nasu shawarwarin a madadin wanda aka gabatar musu ga babban mai shiga tsakani, shugaba Gnassingbe Eyadema na Togo.

Yau makonni biyu ke nan mashawartan gwamnati da na 'yan tawaye suna ganawa domin su yi kokarin kawo karshen fitinar da ta hallaka daruruwan mutane ta kuma raba kasar Ivory coast gida biyu.

XS
SM
MD
LG