Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sufetocin Makamai Na Majalisar Dinkin Duniya Zasu Doshi Iraqi - 2002-11-14


Sufetocin makamai na Majalisar Dinkin Duniya, MDD, suna shirin yin tattaki zuwa kasar Iraqi, domin fara farautar makaman kare dangi, a karkashin wani sabon kuduri mai tsauri da ya bukaci Iraqi ta kwance damarar yaki.

Babban sakataren MDD, Kofi Annan, ya ce sufetocin majalisar zasu fara isa kasar Iraqi a ranar litinin, inda ake sa ran zasu fara aiki cikin makonni kalilan. Ya ce sufetocin sun san abinda zasu yi idan har Iraqi ta ki bada hadin kai.

Tilas ne sufetocin su mika takardar bayanin irin hadin kan da Iraqi take ba su watanni biyu a bayan sun fara farautar makaman.

Jaridar Washington Post ta ce tuni har an mikawa sufetocin jerin wurare fiye da dubu daya da zasu iya bincika su ga ko an boye makamai masu guba, ko na nukiliya a cikinsu.

Amurka ta ce ana iya daukar matakan soja a kan Iraqi idan har shugaba Saddam Hussein ya ki bin umurnin MDD.

Wata jarida mallakar gwamnatin Iraqi ta fito a yau alhamis tana musanta cewa Iraqi tana da makamai na kare dangi. Amma sakataren tsaron Amurka, Donald Rumsfeld, ya shaidawa 'yan jarida cewa lallai Iraqi tana da su, kuma sufetocin zasu gane wa idanunsu.

XS
SM
MD
LG