Musulmi masu zanga-zanga sun kona ofishin wata jarida, a bayan da suka fusata da wani rahoton da jaridar ta buga cewar Annabi Muhammad (saw) yana iya auren daya daga cikin masu takara a gasar sarauniyar kyau ta duniya ta zamo matarsa.
Gungun Musulmi sun yi caa a kan ofishin jaridar "This Day" a garin kaduna yau laraba suna rera wakokin Musulunci yayin da suka kona ginin.
Babu wanda ya ji rauni a wannan lamarin.
Nijeriya tana daukar bakuncin gasar zaben sarauniyar kyau ta duniya ta bana wadda za a yi cikin watan Disamba a Abuja. Wata kungiyar Musulmi mai suna Kungiyar Ulama ta roki shugaba Olusegun Obasanjo da ya hana gudanar da wannan gasa.
A ranar asabar jaridar ta buga labarin cewa Musulmi suna dauka cewar abu ne maras kyau a gayyato mata 92 zuwa Nijeriya domin tallata tsiraiinsu, ta kuma ce ai da wannan zamanin Annabi Muhammad (saw) ne, ta yaya za a dauki wannan batu. Jaridar ta ci gaba da cewa watakila da auren daya daga cikin masu gasar zai yi.
Tuni dai jaridar ta nemi gafarar buga wannan labari.