Akalla mutum guda ya mutu a lokacin da wani abu ya fashe cikin wani dakin ajiye kayayyaki na babban filin jirgin saman Lagos a Nijeriya.
An ce akwai wasu mutanen da wannan lamari ya rutsa da su a cikin dakin wanda ke cin wuta a yanzu haka, yayin da shaidu suka ce sun ga an dauki wadanda suka ji rauni daga wurin. Ba a san yawan wadanda suka ji rauni ba.
An ga wuta da hayaki na fitowa daga wannan gini mai hawa biyu, wanda ke dab da wurin hawa da saukar fasinja. 'Yan kwana-kwana suna wurin a yanzu haka suna kokarin kashe wannan wuta.
Hukumomi ba su bayyana abinda ya haddasa wannan fashewa ta yau alhamis ba. Amma wani jami'in kwastam mai suna Patrick Akpoyipo, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa wata garwar dake kunshe da magungunan kimiyya ce ta fado daga kan wata motar lodin kaya, sai ta yi bindiga ta yada wuta zuwa ga kayayyakin dake cikin dakin.