Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafa Dokar Hana Yawo A Kaduna - 2002-11-21


Hukumomi sun kafa dokar hana yawon dare a garin Kaduna dake arewacin Nijeriya, a bayan da fada ya kara rincabewa mai nasaba da batun gasar sarauniyar kyau ta duniya da za a yi a kasar.

An ce Musulmi matasa sun kona majami'u, suka farfasa kantuna da tagogin motoci yau alhamis a titunan garin na Kaduna.

Shaidu sun ce sun ga gawarwakin da aka kona a kan tituna.

Wannan rikici ya barke jiya laraba a lokacin da wasu Musulmin da suka fusata suka kona ofishin jaridar "This Day" dake unguwar Malalin Kaduna. Musulmin sun fusata ne da wani kalamin batuncin da jaridar ta buga kan Annabi Muhammad (s.a.w) dangane da batun zaben sarauniyar kyau ta duniya. Jaridar dai tuni ta fito tana neman gafarar buga wannan kalami da ta yi.

Shugabannin Musulmi da yawa a Nijeriya sun soki lamirin zaben sarauniyar kyau ta duniyar da za a yi ranar 8 ga watan Disamba a kasar, suna masu fadin cewa irin wannan buki yana daukaka fasikanci.

XS
SM
MD
LG