Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fitinar Da Ake Yi A Nijeriya Ta Bazu Zuwa Abuja, Babban Birnin Kasar - 2002-11-22


Tashin hankalin da ake yi a garin Kaduna dake arewacin Nijeriya kan batun zaben sarauniyar kyau ta duniya ya bazu zuwa babban birnin kasar.

A bayan da aka yi Sallar Jumma'a, Musulmi sun bazu a kan tituna suna nuna rashin yardarsu ta hanyar kona motoci da kantuna tare da kakkafa shingaye.

A yanzu dai an ce komai tsit a garin Kaduna a bayan da a yau da safe matasa mabiya addinin Kirista suka kai farmakin da suka ce na ramuwa ne a kan Musulmi ta hanyar farfasawa da kona Masallatai.

A bayan da aka shafe kwanaki biyu cur ana yin tashin hankali, an kashe mutane fiye da 100, aka raunata wasu akalla 500, yayin da aka ce har yanzu konannun gawarwaki a watse a kan titunan garin.

Fada ya barke a lokacin da Musulmi suka yi zanga-zangar nuna rashin jin dadin wani kalamin batuncin da wata jarida mai suna "This Day" ta buga game da Annabi Muhammad (s.a.w.)

Jami'an dake shirya gasar zaben sarauniyar kyau ta duniya sun ce duk da wannan tashin hankali, za a ci gaba a gudanar da wannan gasa kamar yadda aka shirya a ranar 7 ga watan Disamba.

XS
SM
MD
LG