Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kura Ta Fara Lafawa A Kaduna, Arewacin Nijeriya - 2002-11-23


Kura ta lafa, yayin da al'amuran yau da kullum suka fara komawa kamar yadda aka saba a garin Kaduna dake arewacin Nijeriya, a bayan da aka shafe kwanaki uku ana dauki-ba-dadi a tsakanin Musulmi da Kirista kan zaben sarauniyar kyau ta duniya.

Wakiliyar Muryar Amurka a Kaduna ta ce a yanzu an bude kasuwanni yayin da motocin haya suka koma ga jigilar kamar yadda suka saba.

Wasu 'yan kasuwar da suka tattauna da wakiliyar tamu suka ce tun lokacin da suka bude kantunansu suka fara ciniki, babu wani abu na tashin hankali da suka gani.

Sai dai kuma an ci gaba da gwabza fada jefi-jefi yau asabar a wasu unguwannin dake bayan garin Kaduna.

Tun da fari, masu shirya zaben sarauniyar kyau ta duniya a Abuja, babban birnin Nijeriya, sun bada sanarwar kawar da wannan buki daga Nijeriya baki daya zuwa London a kasar Ingila.

Shugaban Kungiyar agajin Red Cross ta Nijeriya, Emmanuel Ijewere, ya ce wasu gungun Kiristoci sun kai farmaki "mai zafi" a kan unguwannin Musulmi na kudancin garin Kaduna, a saboda suna daukar soke zaben sarauniyar kyau din a zaman nasara ga Musulmi.

Tun da fari dai, hukumomi a jihar ta Kaduna sun rage tsawon dokar hana yawo ta komo daga karfe 8 na dare zuwa 7 na safe.

Mutane fiye da 100 aka ce sun mutu a wannan fada da aka yi a Kaduna, yayin da wasu 500 suka ji rauni.

Musulmin Nijeriya da dama suna yin adawa da zaben sarauniyar kyaun, suna masu fadin cewa yana kara karfafa fasikanci. Jama'ar Musulmi sun kara kufula a bayan da wata jarida ta buga wani kalamin batuncin dake fadin cewa Annabi Muhammad (saw) zai iya zaben daya daga cikin sarauniyar ta zamo matarsa.

XS
SM
MD
LG