Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aikin Binciken Makamai Na Farko Ya Tafi Sumul A Iraqi - 2002-11-27


Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, MDD, Kofi Annan, ya ce an fara gudanar da aikin binciken makamai a kasar Iraqi ba tare da wata tangarda ba. Amma ya sake jaddada cewa tilas ne hukumomin Iraqi su bada cikakkaen hadin kai.

Mr. Annan yayi wannan furuci a cikin hirar da wani gidan rediyon Faransa yayi da shi, jim kadan a bayan da sufetoci suka fara farautar haramtattun makamai a karon farko cikin shekaru hudu.

Sufetocin dake tafiya a cikin kwambar motoci 24 sun kasu gida biyu a bayan da suka bar hedkwatarsu yau laraba da safe.

Kungiya guda ta kwararrun dake farautar makamai masu linzami da na guba, ta zarce zuwa wani makeken barikin sojoji dake wata unguwa a gabashin birnin na Bagadaza.

Kungiyar ta biyu ta jami'ai daga Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya dake binciken masana'antun sarrafa nukiliya na Iraqi, ta wuce zuwa wata karamar masana'anta a arewa maso gabas da Bagadaza.

Jami'an Iraqi dake cikin wasu motoci dabam sun yi rakiya ma sufetocin. 'Yan jarida sun bi bayan kwambar sufetocin, amma ba a kyale su sun shiga cikin sansanonin da sufetocin ke bincike ba.

Jim kadan a bayan da sufetocin suka fita domin fara gudanar da ayyukansu, an ji karar gwarjen da ake hurawa na gargadin mutane cewar ga hari tafiye daga sama a Bagadaza, sannan a bayan mintoci goma aka buga gwarjen dake nuna cewa hadari ya shige. An ambaci wani jami'in tsaron Iraqi yana fadin cewa an buga gwarjen ne a saboda jiragen saman yakin kasashen yammaci sun ratsa ta samaniyar babban birnin na Iraqi.

XS
SM
MD
LG