Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Kare 'Yancin 'Yan Jarida Sun Yi Tur Da wata Fatawa A Nijeriya - 2002-11-27


Kungiyoyin kare hakkin 'yan jarida sun yi tur da kiran da aka yi a Nijeriya na a kashe wata 'yar jarida dangane da wani sharhin da ta rubuta a kan zaben sarauniyar kyau ta duniya wanda ya haddasa mummunan zub da jini.

Kwamitin kare hakkin 'Yan Jarida mai hedkwata a New York, da kuma Kungiyar "Reporters Without Borders" mai hedkwata a birnin Paris duk sun ce bai kamata a yi wa 'yan jarida barazana a saboda abinda suka rubuta ba.

A makon jiya Isioma Daniel, marubuciya kan batutuwan da suka shafi kwalliya irin ta zamani ta rubuta wani sharhi cikin jaridar "This Day" inda take fadin Annabi Muhammad (s.a.w.) zai iya zaben daya daga masu takarar sarauniyar kyau ta duniya ta zamo matarsa. Wannan sharhi nata ya haddasa mummunar fitina inda aka kashe mutane fiye da 200 a garin Kaduna na arewacin Nijeriya.

Jiya talata hukumomi a Jihar Zamafara dake arewacin Nijeriya suka bayar da abinda suka kira "Fatawa" inda suka bukaci Musulmi da su kashe Ms. Daniel. Abokan aikinta sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa ta gudu ta taho nan Amurka.

Gwamnatin Nijeriya ta ce ba zata kyale a kashe matar ba.

XS
SM
MD
LG