Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Faransa Sun Musanta Ikirarin Da Rundunar Sojojin Ivory Coast Tayi Cewar 'Yan Tawaye Sun kai Farmaki - 2002-11-27


Sojojin Faransa dake kula da yadda ake yin aiki da shirin tsagaita wuta a kasar Ivory Coast sun ce ba su ga wata alamar sake gwabza fada ba, duk da zargin cewa 'yan tawaye sun kai farmaki a kan sojojin gwamnati.

Wani kakakin sojojin Faransa, ya ce dakarunsa sun binciki rahoton da kakakin rundunar sojojin Ivory Coast ya bayar, amma kuma ba su ga wata alamar an gwabza fada ba.

Tun da fari a yau laraba, kakakin sojojin Ivory Coast, Jules Yao Yao, ya ce wata kwambar 'yan tawaye ta kai farmaki kan cibiyoyin sojojin gwamnati a gabashin kasar, a wani abinda ya zamo matakin farko na keta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka yi makonni 6 ana aiki da ita a kasar.

A halin da ake ciki, ministan harkokin wajen Faransa, Dominique de Villepin, yayi kiran da a warware rikicin na Ivory Coast cikin lumana. yayi wannan kiran ne a bayan da ya gana da shugaba Laurent Gbagbo a birnin Abidjan.

Har ila yau, Mr. de Villepin ya samu nasarar fitar da shugaban 'yan adawa, Alassane Ouattara daga kasar. Tun lokacin da 'yan tawaye suka fara yin bore a ranar 19 ga watan Satumba, Malam Ouattara ya tare gidan jakadan Faransa a Ivory Coast, abinda ya haddasa zanga-zangar nuna kin jinin Faransa. Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ambaci wani mukarrabin Malam Ouattara yana fadin cewa ya tashi zuwa kasar Gabon.

XS
SM
MD
LG