Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Sabbin 'Yan Tawaye Sun Kunno Kai A Kasar Ivory Coast - 2002-11-29


Sojojin Faransa dake aikin kiyaye zaman lafiya a Ivory Coast sun ce sojojin gwamnati sun komo bayan layin da aka shata na tsagaita wuta a bayan da suka gwabza da sojojin gwamnati a tsakiyar kasar, sai dai kuma gwamnatin tana fuskantar wani sabon tawaye a wasu garuruwa biyu a yammacin kasar.

Wani kakakin sojojin Faransa ya fada yau Jumma'a cewar 'yan tawaye sun kori sojojin gwamnati daga garuruwan Danane da Man a tsakiyar cibiyar noman Cocoa a yammacin kasar. Wani rahoton daga kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce an ga karin sojojin gwamnati masu yawan gaske sun doshi yamma.

An ce wannan sabuwar kungiyar 'yan tawaye ta magoya bayan wani tsohon shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar ne, Janar Robert Guei, wanda sojoji masu biyayya ga gwamnati suka kashe a farko-farkon tawayen kasar a watan Satumba.

Jiya alhamis sojojin gwamnati suka karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka yi makonni 6 ana yin aiki da ita, ta hanyar tsallaka layin da ya raba tsakani domin kai hari kan sojojin 'yan tawaye a garin Vavoua na tsakiyar kasar. Sojojin Faransa masu kula da yadda ake yin aiki da shirin tsagaita wuta sun ce sojojin na gwamnati sun ja da baya a yau Jumma'a.

'Yan kiyaye zaman lafiyar na Faransa sun ce sojojin haya masu tallafawa gwamnati, cikinsu har da turawa da sojoji masu magana da harshen Ingilishi, sun dafawa sojojin Ivory Coast masu magana da harshen Faransanci a fadan na jiya alhamis.

Kama garuruwa biyun da sabbin 'yan tawayen na Ivory Coast suka yi, ya sa a yanzu kasar tana rabe gida uku. Kudancin kasar yana karkashin gwamnati, yayin da akasarin arewacin kasar yake hannun 'yan tawayen da suka fara bore a ranar 19 ga watan Satumba.

XS
SM
MD
LG