Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Ivory Coast Zai Gana Da Takwaransa Na Burkina Faso - 2002-11-30


An bada rahoton cewa shugabannin Ivory Coast da Burkina Faso suna shirin ganawa ranar talata a Bamako, babban birnin kasar Mali, domin tattauna fitinar dake kara yaduwa a kasar Ivory Coast, inda a yanzu ake da kungiyoyin 'yan tawaye biyu.

Wani kakakin shugaba Laurent Gbagbo na Ivory Coast ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa lokaci yayi da ya kamata kasar ta bude sabon babi a dangantaka da makwabtanta.

A can baya, shugaba Gbagbo ya zargi Burkina Faso da laifin tallafawa 'yan tawayen dake rike da yankunan arewacin kasar. Jami'ai a birnin Ouagadougou (Wagadugu) sun ce babu ruwansu da wannan tawaye.

Dubban 'yan kasar Burkina Faso dake zaune a Ivory Coast sun gudu saboda tsoron musgunawa a hannun jami'an tsaro.

Labarin ganawar da shugabannin biyu zasu yi, ya zo a daidai lokacin da gwamnatin Ivory Coast ta tura dakarunta domin kwantar da wutar wani sabon tawayen da ya kunno kai a yankin yammaci, inda ake noman Cocoa mai matukar muhimmanci ga kasar.

Shugabannin 'yan tawaye a yammacin kasar sun ce suna rike da garuruwan Danane da Man. An ce su wadannan 'yan tawayen, masu goyon bayan tsohon shugaban gwamnatin sojan kasar ne, Janar Robert Guei, wanda sojojin gwamnati suka kashe a lokacin da aka fara tawaye cikin watan Satumba.

XS
SM
MD
LG