Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turkiyya Ta Kawo Karshen Dokar-Ta-Bacin Shekaru 15 A Wasu Lardunan Kurdawa Biyu - 2002-11-30


Turkiyya zata kawo karshen dokar-ta-bacin da aka shafe shekaru ana yin aiki da ita a wasu larduna guda biyu na Kurdawa a kasar.

Yau asabar za a kawo karshen mulki da dokar a lardunan Diyarbakir da Sirnak dake kudu maso gabashin kasar, a kusa da bakin iyaka da Iraqi.

Dage dokar-ta-bacin da aka kafa tun shekarar 1987 na daya daga cikin sharrudan da aka gindayawa Turkiyya kafin ta nemi shiga cikin Kungiyar Tarayyar Turai.

Hukumomi a birnin Ankara sun fara sassauto da dokokin kuntatawa al'ummar Kurdawan kasar shekaru ukun da suka shige, lokacin da jam'iyyar Kurdawa 'yan tawaye ta PKK ta bayyana cewa zata daina kai hare-hare, domin ta maida hankali wajen neman 'yancin al'ummar cikin lumana.

XS
SM
MD
LG