Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Kenya Da Amurka Zasu Gana A Washington - 2002-12-02


Shugaba Daniel Arap Moi na kasar Kenya zai gana da shugaba Bush a nan Washington idan Allah Ya kai mu ranar alhamis, mako guda a bayan harin da aka kai kan wani hotel na 'yan Isra'ila tare da wani jirgin saman fasinja, shi ma na Bani Isra'ila a birnin Mombasa.

Aana sa ran shugabannin biyu zasu tattauna batun tsaro a duniya. Shi ma firayim minista Meles Zenawi na Ethiopia zai shiga cikin wannan tattaunawa tasu.

An samu rahotannin sabanin da ya kunno kai a tsakanin masu bincike na Kenya da na Isra'ila kan kula da shaidar da aka samu a wurin da aka kai harin bam din. Jami'an Amurka da na Isra'ila sun ce Kenya ba zata iya gudanar da bincike yadda ya kamata ba.

Amma kuma babban mai bincike a bangaren 'yan Kenya, William Langat, ya ce kungiyoyin suna aiki cikin abota, kuma Kenya ta yarda da rokon Isra'ila na a ba ta damar nazarin kayayyakin shaidar da aka tara daga hare-haren.

Mutane 16 sun mutu a harin kunar-bakin-wake da aka kai kan hotel din 'yan Isra'ila mai suna Paradise a Mombasa, yayin da aka cilla makamai masu linzami biyu kan wani jirgin saman fasinjan Isra'ila dake tashi, amma kuma ba a same shi ba.

XS
SM
MD
LG