Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Hukumar Nijeriya Da Kamaru Ta Fara Ganawa A Yaounde - 2002-12-02


Wata hukumar da Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ta kafa domin taimakawa wajen warware rikicin Nijeriya da Kamaru kan yankin Bakassi, ta fara aikinta a Yaounde, babban birnin Kamaru.

A watan Oktoba kotun duniya ta bai wa Kamaru yankin an Bakassi mai arzikin mai, tana mai dora hujja da wata yarjejeniyar da turawan mulkin mallaka na Jamus da Ingila suka kulla a sheakar 1913.

Amma Nijeriya ta ki yarda da wannan hukumci, tana mai cewa irin wadannan yarjejeniyoyin 'yan mulkin mallaka ba na halal ba ne. Ta ce kusan dukkan mazauna yankin suna daukar kansu a zaman 'yan Nijeriya, kuma tilas ne a bada muhimmanci ga kula da halin rayuwarsu fiye da sha'anin mai.

Shugabannin tawagogin kasashen biyu, ministan shari'a na Kamaru Amadou Ali, da tsohon ministan shari'ar Nijeriya Bola Ajibola, duk sun fada jiya lahadi cewar sun kuduri aniyar warware wannan sabani cikin lumana.

An shirya wannan tattaunawa har zuwa gobe talata.

XS
SM
MD
LG