Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ci gaba Da Farautar Haramtattun Makamai A Kasar Iraqi - 2002-12-02


An ci gaba da farautar makamai yau litinin a kasar Iraqi, yayin da gwamnatin britaniya ta bada wani rahoton dake zargin dcewa gwamnatin Saddam Hussein tana gana azaba wa, tare da kashe, 'yan kasar ta Iraqi.

Sufetocin makamai na MDD sun ziyarci wata cibiyar soja mai suna Karamah a Bagadaza, yayin da wata tawagar MDD ta ziyarci wata masana'antar sarrafa barasa a wajen babban birnin. Kungiyoyin suna farautar makaman nukiliya da masu guba wadanda aka haramta wa Iraqi mallaka karkashin kudurorin MDD.

Tilas Iraqi ta mikawa kwamitin sulhu cikakken bayani na shirye-shiryen kera makamanta nan da ranar 8 ga watan nan na Disamba, watau ranar lahadi mai zuwa. Amurka tayi barazanar kai farmakin soja idan Iraqi ta ki bin umurnin MDD.

Tun da fari a yau litinin, jiragen saman yakin Amurka da na Britaniya dake sintiri a yankunan da aka haramtawa jiragen yakin Iraqi shiga, sun kai hare-hare kan cibiyoyin soja a kusa da Mosul a arewacin kasar, domin maida martani ga abinda suka kira wutar da sojojin Iraqi suka bude musu. A jiya lahadi ma, mazauna yankin kudancin Iraqi sun ce mutane akalla 4 sun mutu a lokacin da jiragen kasashen yammacin suka kai hari a Basra.

A cikin wata wasikar da ya aikewa da babban sakataren MDD, Kofi Annan, ministan harkokin wajen Iraqi, Naji Sabri, ya bayyana harin na jiya lahadi a zaman wani bangare na abinda ya kira ta'addancin rashin imani da ake yi wa Iraqi.

Wadannan al'amura suna zuwa a daidai lokacin da gwamnatin Britaniya take bada wani rahoton da yayi kagen cewa ana keta hakkin bil Adama a Iraqi. Rahoton na Britaniya ya ce shugaba Saddam Hussein shine ke da laifi kai tsaye na keta hakkin da ake yi a kasarsa, ya kuma bada misali na yadda ake ganawa mutane azaba a Iraqi.

XS
SM
MD
LG