Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Tsaron Amurka Ya Kammala Rangadin Arewa Maso Gabashin Afirka - 2002-12-11


A yau laraba sakataren tsaron Amurka, Donald Rumsfeld, ya kammala ziyarar kwanaki biyu, kuma irinta ta farko, a yankin arewa maso gabashin nahiyar Afirka, inda a yau din ya ziyarci 'yar karamar kasar nan ta Djibouti wadda ke da matukar muhimmanci a harkokin tsaron yankin.

Wakilin Muryar Amurka dake tafiya tare da sakataren tsaron, Alex Belida, ya ce ziyarar sa'o'i uku da rabi da Mr. Rumsfled ya kai zuwa Djibouti, ta zo a daidai lokacin da sojojin ruwa na kasa da kasa dake sintiri a ruwayen yankin arewa maso gabashin Afirka suka tsare wani jirgin ruwa dauke da makamai masu linzami samfurin Scud daga Koriya ta Arewa.

Mr. Rumsfeld bai yi wani sharhi nan take dangane da gano makaman ba. Amma a lokacin da yake ziyara a yankin na arewa maso gabashin Afirka kafin a bayyana gano wadannan makamai, ya bayyana irin muhimmancin wannan sintiri da ake yi cikin teku ga yaki da ta'addanci.

Ya lura cewa akwai jiragen ruwan yaki daga kasasahe da dama dake da hannu a ayyukan tsaro cikin teku a dab da kasar Yemen da kuryar ta arewa maso gabashin Afirka. Ya ce a lokuta da dama ana tsare jiragen ruwan da ake tababar abubuwan da suke dauke da su. Kamar yadda ya ce, a wasu lokutan a kan tsare wadannan jirage a zubar ko kuma a lalata, ko a kwace abubuwan da suke dauke da su.

Jami’an Amurka sun ce sun yi imani watakila makaman na Scud sun doshi kasar Yemen ne, kasar da aka yi imanin cewa 'yan ta'adda, cikinsu har da 'yan al-Qa'ida sun buya a ciki. A tashar jiragen ruwan Aden na kasar Yemen ne a watan Oktobar 2000 'yan ta'adda suka kai hari kan jirgin ruwan yakin Amurka mai suna USS Cole, suka kashe mayaka 17.

Akasarin ayyukan yaki da ta'addancin da Amurka da kawayenta suke gudanarwa, suna yi ne daga cibiya guda a kasar Djibouti, wadda ke tsallaken mashigin ruwa daga kasar Yemen. Ma'aikatar tsaron Amurka ta kafa wata runduna ta musamman ta hadin guiwa a yankin arewa maso gabashin Afirka, wadda ke da hedkwata a kasar Djibouti.

A lokacin ziyarar da ya kai a yau laraba, Mr. Rumsfeld ya saurari bayani game da ayyukan sojojin kawance ya kuma gana da sojojin Amurka a sansanin Lemonier. Har ila yau ya tattauna da shugabannin Djibouti.

Wannan ziyarar da Mr. Rumsfeld ya kai Djibouti, ta biyo bayan wadda ya kai zuwa Eritrea da Ethiopia. Sakataren tsaron na Amurka ya bayyana kudurin gwamnatin shugaba Bush na kulla kawance mai dorewa da wadannan kasashe domin yakar ta’addanci a yankin arewa maso gabashin Afirka. Amma kuma ba a bada sanarwar cimma wata sabuwar yarjejeniya ba ta fadada sansanonin sojan Amurka a yankin zuwa Eritrea ko Ethiopia.

XS
SM
MD
LG