Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bangarorin Da Ba Su Yin Ga-Maciji Da Juna A Kwango-Kinshasa Sun Cimma Yarjejeniya - 2002-12-17


Sassan kasar Kwango-Kinshasa mau yakar juna sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar mukamai, suka kafa sabuwar gwamnatin hadin kan kasa.

A yau talata ne gwamnatin Kwango Kinshasa, da kungiyoyin 'yan tawaye da dama, da 'yan adawar siyasa da kungiyoyin al'umma suka cimma wannan yarjejeniya a bayan wata da watanni ana tattaunawa a Pretoria, babban birnin Afirka ta Kudu.

A karkashin wannan yarjejeniya, shugaban Kwango Kinshasa na yanzu, Joseph Kabila, zai ci gaba da zama kan wannan kujera a zaman shugaban rikon-kwarya har zuwa lokacin da za a gudanar da babban zabe nan da kimanin shekaru biyu da rabi. Zaben zai zamo na dimokuradiyya na farko da za a yi a wannan kasa dake yankin tsakiyar Afirka tun lokacin da ta samu 'yanci daga kasar Belgium a 1960.

Shugaba Kabila zai yi aiki tare da mataimakan shugaba guda hudu: daya daga bangaren gwamnati, daya daga 'yan adawar siyasa da kuma biyu daga manyan kungiyoyin 'yan tawaye biyu na kasar.

haka kuma, dukkan bangarorin kasar, ciki har da kungiyoyin al'umma, sun cimma daidaiton ra'ayi kan yadda za a raba mukaman gwamnati. Kungiyar 'yan tawaye mai suna M.L.C. zata rike shugabancin majalisar dokoki ta kasa. Kungiyoyin al'umma kuma zasu zabi shugaban majalisar dattijai.

Har ila yau, yarjejeniyar ta kyale shugabannin 'yan tawaye su yi amfani da dogarawansu masu tsaron lafiya idan sun fara aiki a sabbin mukamansu a Kinshasa.

wata kungiyar tsaron Majalisar Dinkin Duniya da za a fadada, zata taimaka wajen tabbatar da yin aiki da yarjejeniyar.

XS
SM
MD
LG