Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nelson Mandela Ya Soki Manufofin Amurka Game Da Iraqi - 2002-12-17


Tsohon shugaban Afirka ta Kudu, Nelson Mandela, ya sake fitowa yana sukar manufar Amurka game da kasar Iraqi.

A lokacin da yake magana yau talata a wurin taron jam'iyyar ANC mai mulkin Afirka ta Kudu a garin Stellenbosch, Mr. Mandela ya ce a yawancin lokuta, Amurka da Britaniya sukan yi watsi, ta hanya mai hadarin gaske, da abinda ya kira akidar hada kai tsakanin kasashe wajen gudanar da al'amuran duniya.

Tsohon shugaban mai shekaru 84 da haihuwa, ya ce ya kamata sauran kasashen duniya su fito su yi magana idan har Amurka ta take wannan akida.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ambaci Mr. Mandela, wanda ya sha sukar manufofin Amurka, yana fadin cewa Amurkar tana nunawa duniya cewar ita kawai yaki take son kaddamarwa kan kasar Iraqi ta kowane hali.

Duk da sukar manufar Amurka da yake yi, Mr. Mandela ya ce yana daukar kansa a zaman abokin Amurka.

XS
SM
MD
LG