Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohuwar Shugabar Sabiyawan Bosniya Ta Amince Da Cewar An Kashe Dubbai A Kyamfe Din Tsarkake Jinsi - 2002-12-17


Tsohuwar shugabar 'yan kabilar Sabiyawan Bosniya, Biljana (Bilyana) Plavsic, ta yarda cewa dubban mutanen da ba su ji ba, ba su kuma gani ba, sun mutu a sanadin kashe-kashen kare-dangin da Sabiyawa suka yi na ganin bayan sauran kabilun da ba nasu ba a Bosniya.

Ta ce da farko tayi imani da cewa Sabiyawan suna kare kansu ne daga danniya irin wadda aka nuna musu a lokacin yakin duniya na biyu. Ms. Plavsic ta ce daga baya ta gano cewar dubban Musulmi da Kuroshiyawa sun hallaka, kuma babu wata hujja ta gallaza musun da aka yi, a kokarin 'yan kabilar Sabiyawa na korar duk sauran kabilun daga cikin yankunan da suke ikirarin cewa nasu ne.

Tsohuwar shugabar Sabiyawan ta bayyana wannan ne a lokacin da kotun duniya mai bin kadin laifuffukan yaki na Bosniya a birnin Hague take nazarin irin hukumcin da zata yanke mata.

Tun da fari, tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka, Madeleine Albright, ta shaidawa kotun cewa Ms. Plavsic ce ummul haba'sin wasu daga cikin munanan ayyukan da aka tabka a lokacin.

Amma kuma ta yabawa Ms. plavsic a saboda daga baya ta zo ta goyi bayan yarjejeniyar zaman lafiya ta Dayton wadda ta kawo karshen fadan da aka gwabza.

Ms. Plavsic ta amsa laifin da ak tuhume ta da shi guda daya na cin zarafin bil Adama.

XS
SM
MD
LG