Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Fara Girka Makaman Kariya Daga Makamai Masu Linzami - 2002-12-17


Shugaba Bush ya umurci rundunar sojoji da ta fara girka garkuwar kare Amurka daga hare-haren makamai masu linzami nan da shekara ta 2004.

A cikin wata rubutacciyar sanarwa, shugaban ya bayyana girka garkuwar ta farko da za a yi a zaman matsakaiciya, ya kuma ce zata karfafa tsaron Amurka.

Jami'an ma'aikatar tsaron Amurka suka ce shugaban yana shirin girka makaman tarewa da harbo makamai masu linzami guda 10 a sansanin sojoji na Fort Greeley dake Jihar Alaska nan da shekara ta 2004. Suka ce ya zuwa shekarar 2005 ko 2006, za a kara irin wadannan makaman garkuwa guda goma a sansanin.

Da zarar an kafa su, wadannan makamai zasu bai wa sojojin Amurka damar harbo duk wani makami mai linzami mai cin dogon zango da aka harbo a kan Amurka.

Masu sukar girka wannan garkuwa da dubban miliyoyin daloli sun ce kaifinta bai kai yadda har za a iya fara girka ta a yanzu ba.

XS
SM
MD
LG