Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Nguema Ya Sake Lashe Zaben Shugaban Kasar Equatorial Guinea - 2002-12-19


Sakamakon zaben da aka samu daga Equatorial Guinea ya nuna cewa shugaba Teodoro Obiang Nguema, wanda ya jima yana mulkin kasar, shine ya lashe zaben da kashi fiye da 97 daga cikin 100 na dukkan kuri'un da aka jefa.

Shugaban yayi takara shi kadai, a bayan da mutane hudun dake kalubalantarsa suka janye daga zaben na ranar lahadi suna zargin magudi. 'Yan hamayya sun yi kiran da a gudanar da sabon zabe.

Babban dan takara na hamayya, Celestino Bonifacio Bacale, ya ce an hana masu jefa kuri'a kada kuri'unsu cikin sirri. Gwamnati ta musanta wannan. Jami'an zabe suka ce mutane fiye da dubu 200 suka kada kuri'unsu ma shugaba Nguema.

Mr. Obiang Nguema ya hau kan kujerar mulkin wannan kasa mai arzikin man fetur shekaru 23 da suka wuce, a lokacin da yayi juyin mulkin ma kawunsa, Francisco Macias Nguema, wanda daga baya aka gurfanar gaban shari'a aka kuma kashe.

Ana sukar gwamnatin shugaba Obiang Nguema da laifin take hakkin bil Adama, musamman ma yadda take jefa abokan hamayyar siyasarta a kurkuku ta kulle su.

XS
SM
MD
LG