Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amnesty International Tayi Kira Ga Gwamnatin Nijeriya Da Ta Mutunta Hakkin Jama'a... - 2002-12-19


Kungiyar kare hakkin bil Adama ta "Amnesty International" tayi kira ga gwamnatin Nijeriya da ta mutunta hakkin jama'arta, ta kuma hukumta sojojin da ake zargi da laifin kashe daruruwan kauyawa a wasu jihohi biyu.

A cikin wani rahoton da aka bayar yau alhamis, kungiyar mai hedkwata a London ta ce dakarun tsaron Nijeriya sun karkashe mutane ba bisa hanyoyin da shari'a ta tsayar ba, tare da gana azaba da kulle mutane haka siddan. Ta ce da alamun wannan tashin hankalin ya faru ne a bisa sakaci, koma dai da hadin bakin ita gwamnatin.

Amnesty ta ce sojoji sun kashe mutane 450 a jihohin Bayelsa da Binuwai a shekarun 1999 da 2001, domin daukar fansar sojoji da 'yan sandan da aka kashe a wuraren.

Kungiyar kare hakkin bil Adamar ta ce tilas shugaba Olusegun Obasanjo ya tabbatar da cewa wadaznda suka aikata wannan ta'asa sun fuskanci shari'a karkashin dokokin kasa da kasa.

XS
SM
MD
LG