Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zababben Shugaban Koriya Ta Kudu Yana Son A Samu Sauyin Fasalin Dangantakar Kasarsa Da Amurka - 2002-12-20


Zababben shugaban Koriya ta Kudu, Roh Moo-hyun, ya ce yana son a samu sauyi a dangantakar kasarsa da Amurka.

Sa'o'i a bayan da ya lashe zaben shugaban kasar Koriya ta Kudu, Mr. Roh ya shaidawa 'yan jarida a yau Jumma'a cewa ya kamata Amurka da Koriya ta Kudu su ci gaba da zama kawayen juna na kwarai. Sai dai kuma ya kara da cewa lokaci yayi da wannan dangantaka zata sauya fasali.

Mr. Roh ya ce yana son a samu sauyin fasalin sannu kan hankali, amma bai yi karin bayani ba. A lokacin yakin neman zabe, Mr. Roh ya ce zai nemi karin 'yanci daga manufofin Amurka.

Har ila yau, Mr. Roh yayi alkawarin yin aiki tare da Amurka wajen warware rikicin da ake yi game da shirin kera makaman nukiliya na Koriya ta Arewa.

Mr. Roh, dan takarar jam'iyyar dake mulkin kasar a yanzu, ya samu nasara, amma ba da kuri'u masu yawa ba, a kan dan takarar hamayya Lee Hoi-chang. Yakin neman zaben da suka yi, ya zo a daidai lokacin da 'yan Koriya ta Kudu suke kara nuna kin jinin Amurka, a dalilin sakin wasu sojojin Amurka biyu da suka taka wasu 'yan matan Koriya biyu suka kashe su a watan Yuni.

XS
SM
MD
LG