Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alex Ekwueme Ya Ce Zai Kalubalanci Olusegun Obasanjo - 2002-12-20


Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Cif Alex Ekwueme, ya ce zai kalubalanci shugaba Olusegun Obasanjo a zaben share fage na tsayar da dan takara da jam'iyyarsu ta PDP zata yi a wata mai zuwa.

A lokacin da yake bayyana takarar tasa jiya alhamis, Cif Ekwueme ya ce zai yi kokarin hada kawunan 'ya'yan jam'iyyar ta PDP mai mulkin kasar wadanda suka rarrabu, tare da hada kan al'ummar kasar. Nijeriya, kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a doron nahiyar Afirka, ta fuskanci fadace-fadacen kabilanci da suka yi sanadin mutuwar dubban mutane cikin 'yan shekarun nan.

Cif Ekwueme ya ce wannan ne lokaci na dinke barakar jam'iyyar da kuma Nijeriya baki daya. Har ila yau yayi alkawarin fadada tattalin arzikin kasar tare da tabbatar da cewa mutane sun ci albarkacin man fetur da Allah Ya bai wa Nijeriya.

A farkon wata mai zuwa ne jam'iyyun Nijeriya zasu gudanar da zaben tsayar da 'yan takarar kujerar shugaban kasa.

An zabi Mr. Obasanjo a matsayin shugaban Nijeriya a 1999, bayan da sojoji suka mika mulki hannun farar hula. Kafin nan, yayi shekaru 4 yana mulkin kasar a zaman soja daga 1976 zuwa 1979.

XS
SM
MD
LG