Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijeriya Ta Tsayar Da Ranakun Yin Zabe - 2002-12-20


Hukumar zabe mai zaman kanta a Nijeriya, INEC, ta ce za a gudanar da zaben shugaban kasa ranar 19 ga watan Afrilu idan Allah Ya kai mu a kasar.

Zaben zai zamo na farko da fararen hula suka shirya maimakon soja a cikin shekaru 20 da suka wuce.

Hukumar zabe ta ce idan har bukatar haka ta taso, za a gudanar da zaben fitar da gwani mako guda bayan zaben farko, watau idan har babu dan takarar da ya lashe zaben kai tsaye.

Har ila yau, hukumar ta tsayar da ranar 12 ga watan Afrilu ta zamo ranar da za a gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin tarayya, yayin da za a yi zaben 'yan majalisun dokokin jihohi a ranar 3 ga watan Mayu.

Za a yi zaben gwamnoni a ranar da za a zabi shugaban kasa.

Nijeriya ba ta taba mika mulki daga wannan gwamnatin farar hula zuwa wancan ba tun lokacin da ta samu 'yanci daga Ingila a shekarar 1960. Yunkurin da aka yi a can baya, ciki har da na 1983, ya ci tura ko kuma dai ya haddasa sojoji sun kwace mulki.

XS
SM
MD
LG