Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Ivory Coast Zai Gabatar Da Sabon Tayin Shirin Cimma Zaman Lafiya - 2002-12-24


Ana sa ran shugaba Laurent Gbagbo na Ivory Coast zai gabatar da sabon shiri kan hanayr cimma zaman lafiya a kasar dake yankin Afirka ta Yamma, bayan da aka shafe watanni uku da kwanaki ana yakin basasa.

Wani kakakin shugaban ne ya bada wannan sanarwa yau talata, amma bai yi karin bayani ba.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ambaci majiyoyin gwamnati suna fadin cewa shirin ya hada da kafa sabuwar gwamnatin hadin kan kasa, tare da gudanar da kuri'ar raba-gardama kan muhimman batutuwan da suka haddasa wannan rikici na kasar Ivory Coast.

Kamfanin dillancin labaran ya ambaci majiyoyin suna fadin cewa an mika wannan shirin ga gwamnatocin Togo da Faransa, wadanda suke kokarin ganin an cimma zaman lafiya a Ivory Coast.

'Yan tawayen Ivory Coast sun yi watsi da tayin sassaucin da gwamnati ta gabatar a baya, suna masu bukatar sai lallai shugabab Gbagbo ya sauka a kuma gudanar da sabon zabe.

Wannan matakin baya-bayan nan da gwamnatin Ivory Coast ta dauka ya biyo bayan dakatar da shawarwarin neman zaman lafiyar da ake yi a kasar Togo a ranar litinin.

Babbar kungiyar 'yan tawaye mai cibiya a arewacin kasar ta kaddamar da tawaye cikin watan Satumba domin nuna rashin yarda da sallamar wasu sojoji da gwamnati ke shirin yi. Tun lokacin, wasu sabbin kungiyoyin 'yan tawaye guda biyu sun kunno kai a yammacin kasar, suna masu lasar takobin dauko fansar kashe tsohon shugaban gwamnatin mulkin soja, Janar Robert Guei, wanda sojojin gwamnati suka yi.

Ivory Coast ita ce kasar da ta fi kowacce noman Cocoa a duniya. Wannan fada yana barazanar lalata tattalin arzikin kasar.

XS
SM
MD
LG