Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Karar Gwamnatin Amurka Dangane Da Kamawa Da Tsare 'Yan Yankin Gabas Ta Tsakiya A Nan Amurka - 2002-12-25


Wasu Amurkawa wadanda asalinsu Larabawa ne da Iraniyawa, da kuma wasu kungiyoyin Musulmi a nan Amurka sun hada kai suka kai karar hukumar kula da shige da ficen baki ta Amurka da atoni-janar na tarayya, a saboda kamawa da tsare mutane 'yan asalin yankin Gabas ta Tsakiya, wadanda suka yi rajista domin radin kansu karkashin wata dokar da aka kafa da nufin bin sawun mutanen da ake zaton 'yan ta'adda ne.

Dubban mazaje daga kasashen Iran, Iraq, Libya, Syria da Sudan sun je su domin yin rajista a ofisoshin yanki na hukumar kula da shige da ficen baki makon jiya a Jihar California.

An kama daruruwa daga cikinsu, aka jefa su a kurkuku.

A cikin karar da suka shigar jiya talata a gaban wata kotu a birnin Los Angeles, kungiyoyin sun ce tsare mutanen da aka yi ya sabawa doka, sun kuma bukaci da a haramtawa hukumomi daukar irin wannan mataki a nan gaba.

XS
SM
MD
LG