Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Paparoma John Paul Yayi Kiran Da A Samu Zaman Lafiya A Gabas Ta Tsakiya - 2002-12-25


Paparoma John Paul na biyu ya gabatar da hudubarsa ta ranar Kirsimeti yau laraba daga fadar Vatican, inda yayi kiran da a kawo karshen tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.

A lokacin da yake huduba ga dubban mabiya a dandalin Saint Peters, Paparoman yayi kira ga mabiya addinai dabam-dabam na duniya da su taimaka wajen kashe wutar abinda ya kira rikicin dake shirin ruruwa a yankin na Gabas ta Tsakiya, amma bai fito a fili ya ambaci kasar Iraqi ba.

Paparpoma John Paul, mai shekaru 82 da haihuwa, ya roki jama’a a fadin duniya da kada su bari fargabar ta’addanci ta sanya su, su rika dari-darin juna.

XS
SM
MD
LG