An rantsar da madugun 'yan hamayya, Mwai Kibaki, a zaman shugaban kasar Kenya na uku, abinda ya kawo karshen mulkin kusan shekaru 40 na jam'iyyar shugaba mai barin gado Daniel Arap Moi.
Babban alkalin kasar Kenya shine ya rantsar da sabon shugaban a dandalin Uhuru na birnin Nairobi, yayin da daruruwan dubban mutane suka ringa daga tutar tarayyar Jam'iyyun hamayya ta "National Rainbow Coalition."
Shugabannin kasashen Uganda da Tanzaniya da kuma Zambiya, tare da wakilai daga Rwanda da Afirka ta Kudu suna daga cikin manyan bakin da suka halarci wannan buki na rantsar da sabon shugaban.
Mr. Kibaki ya ce babban abinda zai bai wa muhimmanci da zarar ya fara aiki shine yaki da zarmiya da cin hanci. Ya ce gwamnatinsa zata bukaci manyan jami'an gwamnati da su bayyana kadarorinsu ta yadda ba zasu iya satar kudin gwamnati ba.
Har ila yau, sabon shugaban na Kenya yayi alkawarin farfado da tattalin arzikin kasar tare da bude kofofin gwamnati ga jama'a. Ya ce mulki ba aiki ne na yayata kwarjinin shugaban kasa ba.
Hukumar zabe ta Kenya ta ayyana Mr. Kibaki a zaman wanda ya lashe zaben ranar Jumma'a, tana mai fadin cewa babu ta yadda dan takarar jam'iyya mai mulkin kasar, Uhuru Kenyatta, zai iya kawar da ratar da aka ba shi.
Mr. Kibaki ya maye gurbin shugaba Daniel Arap Moi mai barin gado, wanda yayi shekaru 24 yana mulkin kasar, wanda kuma tsarin mulki ya haramtawa sake tsayawa takara.