Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Tayi Tur Da Kashe Amurkawa Uku Da Aka Yi A Yemen - 2002-12-30


Amurka ta yi tur da kashe wasu ma'aikata uku Amurkawa a wani asibitin turawan Mishan a kasar Yemen da wani mai tsattsauran ra'ayin addini yayi.

Kakakin fadar White House, Scott McClellan, ya ce Amurka tana yin tur da kakkausar harshe da wannan kisa, kuma zata yi aiki tare da jami'an Yemen wajen binciken harin.

Jami'an tsaro sun ce wani dan bindigar da ake zaton mai kishin addini ne, ya shiga cikin wannan asibitin da Amurkawa ke gudanar da shi a garin Jibla na kudancin kasar, daga nan ya bude wuta. Wasu jami'an mulki biyu tare da likita guda sun mutu nan take.

An ji rauni ma Ba-Amurke na hudu mai aikin harhada magunguna, rauni mai tsanani a wannan harin.

XS
SM
MD
LG