Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Ta Bukaci Cikakken Bayani Daga Gwamnatin Ivory Coast... - 2003-01-02


Faransa ta bukaci gwamnatin Ivory Coast da ta bayyana mata dalilin da ya sanya ta kai hari jiya laraba da jirgi mai saukar ungulu a kan wani kauyen dake hannun 'yan tawaye, har ta kashe mutane 11.

Sojojin Faransa dake Ivory Coast sun ce wannan harin da sojojin gwamnati suka kai a yankin tsakiyar kasar ya keta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka yi watanni biyu da rabi ana aiki da ita.

Gwamnatin Ivory Coast dai ta ce ta auna cibiyoyin sojan 'yan tawaye ne, ba na fararen hula ba, a wannan harin.

Wani kakakin sojan Faransa ya ce wannan lamari ne mai tsanani, wanda kuma zai iya haifar ad sakamakon da ba a zata ba.

Wani kakakin gwamnatin Ivory Coast ya nace kan cewa wannan hari na mayar da martani ne, a bayan da 'yan tawaye suka kai farmaki kan sojojin gwamnati.

A halin da ake ciki, wata kungiyar 'yan tawayen a yammacin Ivory Coast ta fada jiya laraba cewar ta kwace wani kauye mai suna Neka ba tare da fada ba a kusa da bakin iyakar kasar da Liberiya. Rahotanni sun ce 'yan tawaye, wadanda a bisa dukkan alamu suka tsallaka daga Liberiya, sun wawashe kayan mutane a kauyen. Kama wannan kauye ya kusantar da 'yan tawayen ga tashar jiragen ruwan San Pedro, ta biyu wajen girma a kasar.

XS
SM
MD
LG