Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PDP Ta Sake Tsayar Da Obasanjo Yayi Mata Takarar Shugaban Kasa - 2003-01-06


Wakilan jam'iyyar dake mulkin Nijeriya sun fito da gagarumin rinjaye suka zabi shugaba Olusegun Obasanjo a matsayin dan takararsu a zaben shugaban kasar da za a yi cikin watan Afrilu.

Jami'an jam'iyyar PDP suka ce Cif Obasanjo, ya lashe kashi 77 daga cikin 100 na kuri'un da aka jefa a zaben jiya lahadi. Mutumin da ya zo na biyu, tsohon mataimakin shugaban kasa Alex Ekwueme, ya samu kashi 18 daga cikin 100 na kuri'un.

Wakilai suka ce Cif Obasanjo ya samu wannan nasara ce kawai a saboda goyon bayan da ya samu ana dab da wannan zabe daga wurin mataimakinsa, Alhaji Atiku Abubakar. Mataimakin shugaban kasa, wanda ya fito daga arewacin kasar inda Musulmi suka fi yawa, ya fuskanci matsin lamba a kan lallai sai dai ya fito ya kalubalanci shugaban.

A yanzu, ana ganin tamkar Cif Obasanjo yana da kyakkyawar dama ta lashe wa'adi na biyu a zaben da za a yi a ranar 19 ga watan Afrilu, zaben farko da fararen hula zalla zasu gudanar a Nijeriya cikin shekaru 20.

XS
SM
MD
LG