Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Yammacin Ivory Coast Sun Kai Hari Kan Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya Na Faransa - 2003-01-06


Wata kungiyar 'yan tawaye dake rike da wasu yankunan yammacin kasar Ivory Coast ta kai hari kan sojojin kiyaye zaman lafiya na Faransa a kusa da garin Duekoue, cibiyar noman Cocoa.

Wani kakakin sojojin Faransa, ya ce a yau litinin 'yan tawayen suka kai farmaki kan sansanoni biyu na 'yan kiyaye zaman lafiyar dake wannan gari a dab da bakin iyakar kasar da Liberiya. Faransawar sun ce sun mayar da wuta, amma kuma ba su da wani labari na rauni ko mutuwa.

Wani madugun 'yan tawayen yammacin kasar, Felix Doh, ya ce ya bada umurnin kai wannan farmakin ne a saboda sojojin gwamnati sun kai musu hari jiya lahadi. Gwamnati ta musanta cewar tana da hannu a duk wani farmaki.

kakakin sojojin na Faransa ya bayyana wannan lamari a zaman mai tsanani, amma kuma ya ce ba keta haddin yarjejeniyar tsagaita wuta ba ce da aka cimma cikin watan Oktoba, a tsakanin gwamnatin Ivory Coast da babbar kungiyar 'yan tawayen dake rike da yankunan arewacin kasar. 'Yan tawaye na yammacin kasar ba su daukar kansu a zaman wani bangare na wannan yarjejeniya.

A ranar asabar, gwamnatin Ivory Coast da 'yan tawayen arewacin kasar sun yarda zasu gana ranar 15 ga watan nan na Janairu a birnin Paris, domin tattaunawa da nufin kawo karshen watanni ukun da aka yi ana gwabza fada. A jiya lahadi, su ma 'yan tawayen yammacin kasar sun ce a shirye suke su halarci wannan taron.

XS
SM
MD
LG