Koriya ta Arewa ta bada sanarwar janyewa nan take daga yarjejeniyar dakile yaduwar makaman nukiliya a duniya.
Koda yake Koriya ta Arewa zata janye daga wannan yarjejeniya dake neman hana bazuwar makaman nukiliya a duniya, wata sanarwar da hukumomi a birnin Pyongyang suka bayar a yau ta ce kasar ba ta da niyyar kera makaman nukiliya.
Amma kuma wakilin Muryar Amurka a yankin ya ce ana daukar wannan mataki na Koriya ta Arewa a zaman abinda ya kara dagula wannan rikici ya maida shi mai tsananin gaske.
Wannan mataki na yau ya zo a daidai lokacin da wasu ma'aikatan jakadanci biyu na Koriya ta Arewa suke ganawa a nan cikin Amurka da tsohon jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Bill Richardson, wanda a can baya ya kai ziyarce-ziyarcen diflomasiyya zuwa Koriya ta Arewa.
Ana ci gaba da wannan tattaunawa ta su a yanzu haka.