Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Wasikar Da Aka Ce Bin Laden Ya Rubuta Tayi Kira Ga Musulmi Da Su Abokan Gaba - 2003-01-20


Wata jaridar harshen larabci da ake bugawa a London ta wallafa wata wasikar da aka ce Osama bin Laden ne ya rubuta, wadda ke yin kira ga Musulmi da su daina fada da junansu, su hada kai wajen fuskantar wadanda ke kai hare-hare a kan kasashen Musulmi.

Wannan wasikar da aka buga cikin jaridar Asharq al-Awsat a jiya lahadi ta yi kira ga Musulmi da su farka daga barcin da suka jima suna yi, su far ma abokan gaba maimakon junansu.

Akwai kungiyoyin Musulmin dake gaba da junansu a kasashe da dama.

Jaridar ta ce Osama bin Laden ne ya sanya hannu a kan wannan wasika mai shafi 26, kuma an same ta, ta hannun wata cibiyar bincike ta Musulunci dake Pakistan wadda ke da alaka sosai da kungiyar ta'addanci ta al-Qa'ida da bin Laden ke jagoranci.

Wasikar ba ta yi barazana ga wata kasa takamammiya ba. Amma kalamun da Osama bin Laden da sauran shugabannin al-Qa'ida suka yi a can baya sun zargi Amurka da Bani Isra'ila da laifin kaddamar da yakin murkushe Musulmi a duniya.

XS
SM
MD
LG