Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ta Kama 'Yan Koriya Ta Arewa Masu Neman Mafaka - 2003-01-20


Wata kungiyar agaji ta kasa da kasa ta ce 'yan sandan China sun kama 'yan Koriya ta arewa masu yawa dake neman mafaka.

Wata sanarwar da kungiyar mai suna "Doctors Without Borders" ta bayar, ta fada a yau litinin cewa 'yan sanda sun kama 'yan Koriya ta Arewa su 48 da suka buya cikin China, tare da 'yan agaji su 3 dake kokarin taimaka musu domin tserewa zuwa wasu kasashen a cikin kwale-kwale.

An kama wadannan mutane ranar asabar a birnin Yantai dake arewa maso gabashin China. 'Yan rajin kare hakki suka ce watakila za a mayar da wadannan 'yan Koriya ta Arewa zuwa kasarsu mai fama da talauci, inda zasu iya fuskantar dauri a kurkuku tare da azaba.

XS
SM
MD
LG