Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Ta Roki 'Yan Tawayen Ivory Coast Da Su Mutunta Shirin Tsagaita Wuta - 2003-01-22


Faransa ta roki kungiyoyin 'yan tawaye na kasar Ivory Coast da su mutunta shirin tsagaita wuta, a yayin da aka shiga wani mataki mai muhimmanci a tattaunawar neman zaman lafiyar da ake yi a kusa da birnin paris.

Jami'an soja na kasar Ivory Coast suka ce 'yan tawaye sun kaddamar da wani farmaki yau laraba daga cikin kasar Liberiya, inda suka aika daruruwan mayaka zuwa garin Toulepleu a yankin da ake noman Cocoa.

Gwamnati ta ce an kashe mutane 29, ciki har da 'yan Liberiya da dama. Amma dai babu wata kafar da ta gaskata wannan labarin.

An bada rahoton cewa 'yan tawayen Liberiya suna dafawa 'yan tawayen yammacin Ivory Coast a wannan fada da ake gwabzawa. A kwanakin baya Liberiya ta zargi 'yan tawayen da laifin kai hari kan kauyukanta daga sansanoni a cikin Ivory Coast.

A jiya talata, an raunata sojojin Faransa biyu a gwabzawa da 'yan tawayen yammaci kusa da garin Duekoue. daya daga cikin sojojin na Faransa sai da aka yanke masa hannu a saboda tsananin raunin da ya samu. An bada rahoton kashewa ko raunata 'yan tawaye 8.

A wajen tattaunawar da ake yi a Faransa, 'yan tawaye sun bukaci da a gudanar da sabbin zabubbukan da zasu hada da 'yan takarar da aka hana su shiga zaben a can baya bisa hujjoji na dokokin zamowa dan kasa kawai, ciki har da madugun 'yan adawa mai farin jini, Alassane Ouattara.

Shugaban majalisar dokokin Ivory Coast, Mamadou Koulibaly, haka kwatsam ya shura takalmi ya bar zauren taron a makon nan, yana mai zargin Faransawa masu shiga tsakani da laifin nuna goyon baya ga 'yan tawayen.

XS
SM
MD
LG