Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Faransa ya Bukaci Shugaban Ivory Coast Da Ya Rungumi Yarjejeniyar Zaman Lafiyar Da Aka Rattabawa Hannu... - 2003-01-28


Shugaba Jacques Chirac na Faransa yayi kira ga shugaba Laurent Gbagbo na Ivory Coast da ya rungumi yarjejeniyar zaman lafiyar da aka rattabawa hannu kwanakin baya, yayin da rundunar sojojin kasar take cewa ita kam ba ta yarda da wani muhimmin bangare na wannan yarjejeniya ba.

A (jiya) talatar nan rundunar sojojin Ivory Coast ta aike da wasika ga shugaba Gbagbo, tana mai fadin cewa ba ta yarda da sanya 'yan tawaye a cikin gwamnatin hadin kan kasa ba, daya daga cikin muhimman tanade-tanaden wannan yarjejeniya.

Har ila yau wannan yarjejeniya da Faransa ta shiga tsakani aka cimma, ta tanadi cewa shugaba Gbagbo zai mika ikon zartaswa mai yawa ga sabon Firayim Minista, Seydou Diarra, Musulmi daga arewacin kasar.

A makon jiya sassan na kasar Ivory Coast masu fada da juna suka cimma wannan yarjejeniya ta raba iko a lokacin tattaunawa a birnin Paris. Shugaba Gbagbo ya amince da yarjejeniyar ya koma birnin Abidjan a daidai lokacin da magoya bayansa da suka fusata suka bazu kan tituna domin zanga-zangar nuna rashin yarda da wannan yarjejeniya.

Wannan zanga-zanga da aka shiga rana ta biyar da farawa, ta fara rikidewa zuwa ga fitina. Mr. Gbagbo yayi rokon da a kwantar da hankula, kuma a yanzu ya fara bayyana wannan yarjejeniya a zaman "jerin shawarwari" kawai. Ana sa ran zai yi jawabi ga al'ummar kasar, inda zai bayyana dalilan amincewa da yarjejeniyar.

Tun fari a jiya talata, sai da shugaba Chirac na Faransa ya roki shugaba Gbagbo da ya mutunta yarjejeniyar.

XS
SM
MD
LG