Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Majalisar Dokokin Kasar Malawi Sun Jingine Batun Sauya Tsarin Mulki - 2003-01-29


'Yan majalisar dokoki a kasar Malawi sun jingine batun yin gyara ga tsarin mulkin ta yadda shugaban kasar zai iya sake tsayawa takarar neman wa'adi na uku na shekaru biyar kan karagar mulki.

Ministan shari'a, Henry Dama Phoya, ya shaidawa 'yan majalisar dokoki jiya talata a birnin Lilongwe cewar an dage shirin jefa kuri'a kan shirin har sai illa ma sha Allahu.

'Yan adawa sun yi ta sowar yin tur, suna masu bukatar da lallai a jefa kuri'ar a lokacin. Shaidu sun ce an bai wa hammata iska a cikin zauren majalisar, har sai da aka kira 'yan sanda domin kwantar da kura.

'Yan adawa suka ce gwamnati ta janye kudurin ne saboda ta tabbatar da cewa zata sha kaye.

Tun da fari a jiya talatar, sai da shugaba Bakili Muluzi ya kori ministan kasuwanci da masana'antu, Peter kaleso, wanda ya ce zai jefa kuri'ar rashin yarda da kudurin. Ya kuma shaidawa 'yan jarida cewa kudurin ba ya da goyon bayan da za a iya zartas da shi.

Majalisar dokokin Malawi ta ki yarda da matakan da jam'iyya mai mulkin kasar, UDF, ta dauka har akalla sau biyu a can baya da nufin tsawaita wa'adin shugaba Muluzi a kan karagar mulkin kasar. An ambaci shugaban yana fadin cewa yana bukatar karin lokaci kan gadon mulki domin sake fasalin kasar ta Malawi.

XS
SM
MD
LG