Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Zai Nemi Kwamitin Sulhun MDD Ya Gana Ranar 5 Ga Watan Fabrairu - 2003-01-29


Shugaba Bush ya ce zai bukaci Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya da ya gana ranar 5 ga watan Fabrairu, domin abinda ya kira "nazarin matakan rainin ad Iraqi take ci gaba da yi wa duniya."

A cikin jawabinsa na shekara na halin da kasa take ciki, Mr. Bush ya ce sakataren harkokin waje Colin Powell zai gabatar da bayanan leken asiri a game da shirye-shiryen kera haramtattun makamai an Iraqi, da kokarinta na boye su ga sufetocin MDD da kuma alakarta da kungiyoyin 'yan ta'adda.

Mr. Bush ya ce sojojin Amurka dake hallara yanzu haka a Gabas ta Tsakiya zasu fuskanci mawuyacin lokaci a nan gaba. Amma kuma ya ce sojojin na Amurka zasu samu galaba, su samar da abinci da magunguna da kuma 'yanci ga al'ummar Iraqi.

Har ila yau, Mr. Bush yayi amfani da wannan jawabi na shekara-shekara domin tabo muhimman batutuwa na cikin gida, ciki har da bunkasa tattalin arziki ta hanyar rage haraji, da sake fasalin ayyukan kiwon lafiya.

A martanin da suka mayarda ga jawabin an shugaba Bush, 'yan jam'iyyar Democrat sun ce Amurka dai ta doshi mummunar al-Qibla a yanzu. Gwamnan Jihar Washington, Gary Locke, shi ya gabatar da jawabin na 'yan Democrat inda yake cewa shirin farfado da tattalin arzikin shugaba Bush, shakulatin bangaro ne kawai.

Gwamna Locke ya ce shirin na Mr. Bush zai kirkiro da gibin kasafin kudi mai yawa, kuma na dindindin, yayin ad ba zai tabuka komai ab wajen farfado da tattalin arzikin Amurka dake tafiyar hawainiya.

Mr. Locke ya ce suna goyon bayan matakan da shugaba Bush ya dauka na yin aiki tare da MDD kan batun Iraqi. Ya roki shugaban da kada ya nemi cewa lallai sai Amurka ta yi gaban kanta wajen far ma Iraqi, yana mai fadin cewa Amurka ta fi karfi idan ta hada kai da sauran kasashe.

XS
SM
MD
LG