Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Zai Halarci taron Du'a'in Tunawa Da 'Yan Sama Jannatin Columbia... - 2003-02-03


Fadar White House ta ce shugaba Bush zai halarci wani taron du'a'in da za a yi gobe talata domin tunawa da 'yan sama jannatin jirgin jigilar kimiyya na Columbia a Cibiyar Binciken sararin Samaniya ta Johnson dake Houston a Jihar Texas.

Kakain fadar ya ce shugaba Bush yayi imani da cewa wannan bala'i ya taba rayuwar kowane Ba'amurke, kuma ya tunatar da duniya irin hadarin dake tattare da binciken samaniya.

A jiya lahadi, Mr. Bush ya halarci tarurruka a majami'u bayan da ya tattauna ta wayar tarho da iyalan 'yan sama jannatin da suka mutu.

Har ila yau, ya tattauna ta wayar tarho da firayim minista Atal Behari Vajpayee na Indiya dangane da hadarin na Columbia. Mr. Vajpayee musamman wannan hadarin ya jijjiga su a saboda daya daga cikin 'yan sama janntin, Kalpana Chawla, haifaffiyar kasar Indiya ce.

Ita ma Isra'ila ta tabu da wannan bala'i, wanda ya kashe adn sama janntinta na farko.

XS
SM
MD
LG