Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ci Gaba Da Gwabza Fada Tsakanin Wasu Kabilu Biyu A Kudancin Nijeriya - 2003-02-03


Mutane kimanin 12 ne suka mutu a ci gaba da fadan kabilancin da ake gwabzawa game da shirin tsayar da 'yan takarar zaben majalisar dokoki a kudancin Nijeriya.

fada ya sake gocewa jiya lahadi tsakanin 'yan kabilar Urhobo da Itsekiri a garin warri. Wannan fada ya fara tashi ranar Jumma'a a lokacin da jam'iyyar PDP mai mulkin Nijeriya take gudanar da aikin zaben 'yan takararta na majalisar dokoki a garin.

Yayin da hukumomi suka samu nasarar shawo kan wannan fada ranar asabar, sai kuma a jiya lahadi aka sake gocewa da bai wa hammata iska gadan-gadan.

An shirya gudanar da zabubbuka na kasa a Nijeriya, kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a Afirka, a watannin Afrilu da Mayu na wannan shekara. Wadannan kabilu biyu dai tun cikin sheakrun 1990 suka fara gwabza fada da juna a lokacin da wani rikici ya barke har aka kashe mutane fiye da 100 duk a musabbabin inda za a kafa hedkwatar wata karamar hukuma.

XS
SM
MD
LG